flag of Nigeria The Book of Common Prayer
United States England Scotland Ireland Wales Canada World

 
   

Addu’a ta Safiya
Morning Prayer in Hausa (1908)


 

Hausa is a major Chadic language spoken by about 25,000,000 people primarily in Niger and northern Nigeria. It is also a trade and second language for many more people in those and surrounding countries. The language today is usually written in an alphabet based on Latin (as is presented here, but with an additional 3 or 4 letters).

This first translation into Hausa of Morning Prayer, along with several Psalms and the Ten Commandments, was followed by more substantial translations of the Book of Common Prayer:

Karamin Littafin Addu’a.
London: Society for Promoting Christian Knowledge, 1949. (Griffiths 49:4)

Littafin Addu’a.
London: Society for Promoting Christian Knowledge, 1968. (Griffiths 49:5)

Littafin Addua.
Preface signed by Benjamin Argak Kwashi.
Jos: Pastoral Publication of the Anglican Diocese of Jos, 1996.

William Muss-Arnolt discusses missionary work and this early translation into Hausa in Chapter LIX of The Book of Common Prayer among the Nations of the World (1914); this translation is not listed in David Griffiths’s Bibliography of the Book of Common Prayer 1549-1999, but may be the book referred to as his 49:2. This book also contains several Psalms and Hymns, and the ten commandments, which are not given here.

Hausa missionaries
Charles Henry Robinson (1861-1925) and Graham Wilmot Brooke (1865-1892), two early missionaries to Hausa-speaking regions of what is now Nigeria.


 

Thanks are due to Richard Mammana, who transcribed the text, and to Thomas Rae, who provided a copy of the text.

ADDU’A TA SAFIYA

 

 

[PORTIONS OF THE BOOK OF COMMON PRAYER
AND HYMNS IN THE HAUSA LANGUAGE]

 

 

 

SOCIETY FOR PROMOTING CHRISTIAN KNOWLEDGE
LONDON: NORTHUMBERLAND AVENUE, W.C.
1908.


 

 

ADDU’A TA SAFIYA

    Lokachinda mugun mutum ya juyo ga barin muguntassa da ya aikata, yana yin abin da ke halal da daidai kuma, za ya chere da ransa.
    Na dauki swabi-swabina, zunubina yana gabbana tutut.
    Ka kawasda fuskarka dagga wojen zunubina, Ka shafi muguntaina duka.
    Sadakokin Allah kariyeyen ruhu ne: kariyeyar zuchiya mai-tuba, ba za ka rena ta ba, ya Allah.
    Ya Ubangiji ka tsauta ni, amma da shari’a, ba tare da fushinka ba, domin kadda ka wofinta ni.
    Ku tuba, gamma mulin samma ya yi kusa.
    In tashi, in taffi wurin ubana, in che masa, Ya Uba, na yi zunubi a-gabban samma, a-gabbanka kuma, ban issa da za a-kara che da ni danka.
    Kadda ka shiga shari’a gamme da bawanka, Ya Ubangiji; gamma a-wurinka ba mutum mai-rai wanda za shi barata.
    Idan mun che ba mu da zunubi, ruden kanmu mu ke yi, gaskiya kwa ba ta chikkinmu ba: amma idan mum fadi zunubanmu, shi mai-alkawali ne, mai-adilchi, garin shi gafarta mamu zunubanmu, shi tsarkake mu dagga dukan rashin adilchi.

GALGADI

    Yan-uwa ma-sowa kwarai, Litafi mai-tsarki, nasi wuri wuri, yana nufinmu mu dauki zunubanmu da muguntanmu masu-yawa, mu fade su, kadda my yi rikichi, kadda muy rufe su a-gabban sukfar Allah, Mai-iko duka, Ubanmu na samma; amma mu fade su da zuchiya mai-muminanchi, mai-tawali’u, mai-tuba, mai-bibeya: domin mu sami gafarassu, bissa ga nagartassa da jinkansa marasa-iyaka. Ko da shi ke kuma wajib ne a-garemu mu dauki zunubanmu da muminanchi kowanne loto a-gabban Allah, bale fa sa’anda mu kan taru, garin yin godiya sabada alherai masu-girma wadanda mun karba dagga hanuwansa, garin bayannawar yabonsa mai-ishi, garin jin Maganatasa mai-tsarki, garin rokon abin da mu ke bukata ga rai duk da jiki. Domin wannan ina rokonku, ina kwa bida gareku, iyakar wadanda ku ke nan wurin, ku zo tare da ni, da zuchiya mai-tsarki, da muriya mai-muminanchi zuwa kursiyi mai-alheri na samma, tare mu che:—
 

Morning Prayer

FADIN ZUNUBI

    Ya Uba mai-iko duka mai-yawan jinkai: mun ratse, mun bache dagga tafarkokinka kamman batatun tumaki. Mun chikka bin dabarun zukatanmu da muradinsu. Mun swaba dokokinka masu-tsarki. Abin da ya wajabba garemu, mun bari: Abin da ya wajabba mu bari, shi mun yi; Babu lafiya garemu. Amma, Ya Ubangiji, ka yi mana jinkai, mu masu-swabo abin tausai. Ya Allah ka rufi masu-fadin laifinsu, Masu-tuba kwa ka maishe su: bissa alkawalin da ka furta ma yan Adam chikkin Almasihu Isa Ubangijinmu. Ya Uba kuma, mai-yawan jinkai, ka sa nan gabba sabili da shi, mu yi ranmu mai-ibada, mai-adilchi, mai-natsuwa, domin a-girmama sunanka mai-tsarki. Amin.

KWANCHEWAR ZUNUBAI

    Ya Allah mai-iko duka, Uban Ubangijinmu Isa Almasihu, wanda ba ya so mutuwar mai-zunubi ba, amma ya fi son shi juyo ga barin muguntassa, shi yi rai; Ya bada iko da umurni ga masu-bautansa su furta, su fadi kuma ga mutanensa da su ke tuba kwanchewa da gafarar zunubansu. Allah ke gafartawa, yana kwanchewa dukan masu-tuba da gaskiya, masu-bada gaskiya ga bisharassa mai-tsarki ba da munafunchi ba. Domin wannan fa mu roke shi shi ba mu tuba mai-gaskiya, da Ruhunsa Mai-tsarki, domin abubuwan da mu ke yi yanzu su gamshe shi; kuma sauran ranmu da ke nan gabba shi yi tsabta da tsarki, domin hakkanan a-karewa mu zo chikkin farinchikkinsa na har abada, ta wurin Isa Almasihu Ubangijinmu. Amin.
 

Confession & Absolution

ADDU’AR UBANGIJI

    Ubanmu wanda ke chikkin Samma, a tsarkake sunanka, mulkinka shi zo, abin da ka ke so a-yi shi, chikkin duniya kammar yada a-ke yinsa chikkin samma. Ka ba mu rananga abinchin yini. Ka gafarta mana laifinmu, kammar yada muna gafarta ma wadanda su ke yi mamu laifi. Kadda ka kai mu wurin jaraba, amma ka cheche mu dagga Shaitan. Gamma mulki, da iko da girmo naka ne, har abada. Amin.

    Malami. Ka budi lebunmu, Ya Ubangiji.
    Amshi. Bakinmu kwa za ya bayanna yabonka.
    Malami. Ya Allah, ka yi samli garin chetonmu.
    Amshi. Ya Ubangiji, ka yi hamzari garin taimakonmu.
    Malami. Alhamdu ga Uba, da Da da Ruhu Maitsarki.
    Amshi. Kammar yada ya ke a-farko da yanzu, hakkanan kuma har abada, ba matuka. Amin.
    Malami. Ku yi ma Ubangiji yabo.
    Amshi. Sunan Ubangiji shi zamma yababe.

VENITE

    1 Ku zo, mu raira waka ga Ubangiji: mu daukaka muriya da farin-chikki ga pa na chentonmu.
    2 Mu zo gabba gareshi da godiya, mu daukaka muriya ta farin-chikki gareshi da raira wakoki.
    3 Gamma Ubangiji Allah ne mai-girma, Sarki ne baba bissa dukan alloli.
    4 A-chikkin hanunsa zurfafan wurarin duniya su ke; tsawawan duwatsu kuma nasa ne.
    5 Bahar nasa ne, shi kwa ya yi shi; hanuwansa suka kammanta sandarariyar kassa.
    6 Ku zo, mu yi sujadda mu yi ruku’u, mu yi durkussa gabban Ubangiji Ma-halichinmu:
    7 Gamma shi Allahnmu ne, mu mutanen makiyayatasa ne, tumakin hanunsa. Yo, da za ku ji muriyata!
    8 Kadda ku kekashi zuchiyarku, kamman chikkin Mariba, kamman chikkin ranar Massa a-jeji:
    9 Lokachinda ubanninku suka gwoda ni, suka auna ni, suka ga aikina.
    10 Shekara arbaïn ina bakin-chikkin da wannan tsara, na che, Wannan iri ne mai-ratsewa a-chikkin zuchiyarsu, ba su san tafarkokina ba;
    11 Domin wannan na yi rantsuwa chikkin hushina, Ba za su shiga chikkin hutuna ba.
    Alhamdu ga Uba, da Da da Ruhu Mai-tsarki.
    Kammar yada ya ke a-farko da yanzu, hakkanan kuma har abada, ba matuka. Amin.

TE DEUM

    Muna yabonka Ya Allah: mun dauki chewa kai ne Ubangiji.
    Dukan duniya tana yi maka sujadda: Uba Ma-dawami.
    A-gareka Malaïku duka suna tada muriya: da Sammai da Ikoki duka da ke chikkinsu.
    A-gareka Charubin da Sarafin: kullayomi suna tada muriya.
    Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki: Ubangiji Allah Mai-runduna.
    Samma da kassa chikke su ke da Sarautal darajakka.
    Jama’a mai-daraja ta Mazaninka: tana yabonka.
    Ma-nagarchin zumunta ta Annabawa: tana yabonka.
    Jama’a mai-daraja ta Masu-shahada: yana yabonka.
    Ekklisiya mai-tsarki chikkin dukan iyakar duniya: tana shaidanka:
    Ya Uba mai-sarauta mara-iyaka:
    Danka kuma mai-girma, mai-gaskiya, ma-kadaichi:
    Ruhu Mai-tsarki kuma: Mai-taimako.
    Kai ne Sarkin Daraja: Ya Almasihu.
    Kai ne Da ma-tabachi na Uba.
    Sa’anda ka dauka ma kanka ka chechi mutane, ba ka yi kyamar chikkin buduruwa ba.
    Sa’anda ka yi nassara da zafin mutuwa, ka budi Mulkin Samma ga masu-bada gaskiya duka.
    Kana zamne ga hanun dama na Allah: a-chikkin darajar Uba.
    Muna bada gaskiya za ka zuwa: Ka zamma mai-shari’anmu.
    Muna rokonka fa, ka taimaki bayinka: wandanda ka panshe su da jininka mai-daraja:
    Ka maishe su a-chikkin lisafin tsarkakanka, a-chikkin daraja ta har abada.
    Ya Ubangiji ka chechi jama’arka, ka sa ma gadonka albarka.
    Ka malke su: ka daggadda su har abada.
    Yo da gobe muna girmama ka;
     Muna sujadda ga sunanka kuma kullum ba matuka.
    Ya Ubangiji da yardarka ka tsare mu yo banda zunubi.
    Ya Ubangiji ka yi mana jinkai: ka yi mana jinkai.
     Ya Ubangiji ka bar jinkanka shi jido mana: da shi ke bangaskiyarmu tana gareka.
    Ya Ubangiji, a-gareka na bada gaskiya, kadda ka bar ni in rude har abada.

JUBILATE

    1 A-daukaka muriya ga Ubangiji da murna, ya duniya duka.
    2 Ku bauta ma Ubangiji da farin-zuchiya: ku zo gabbansa da rairawa.
    3 Ku sani Ubangiji shi ne Allah: shi ne ya yi mu, ba mu da kanmu ba ne; mu mutanensa ne, tumakin ma-kiyayatasa kuma.
    4 Ku shiga chikkin kofofinsa da abin godiya, achikkin gidajensa kuma da yabo; ku yi masa godiya, ku albarkachi sunansa.
    5 Gamma Ubangiji nagari ne: jinkansa yana tabatta har abada: aminchinsa kuma har zamani duka.
    Alhamdu ga Uba, da Da da Ruhu Mai-tsarki.
    Kammar yada ya ke a-farko da yanzu, hakkanan kuma har abada, ba matuka. Amin.
 

Lord's Prayer

BANGASKIYA

    Ina bada gaskiya ga Allah Uba Mai-iko duka, Mai-halitan samma da kassa.
    Ina bada gaskiya ga Isa Almasihu Dansa ma-kadaichi Ubangijinmu, Wanda aka-habila dagga Ruhu Mai-tsarki ne, Haifuwatasa dagga buduruwa Maryamu, Ya sha wohalla chikkin zamanin Bunti Bilatus, Aka-sa shi ga gichiya, Ya mutu, Aka-yi masa kushewa, Ya taffi Hades: Rana ta uku ya tashi kuma dagga matatu, Ya hawo bissa chikkin samma, Yana zamne ga hanun dama na Allah Uba Mai-iko duka: Dagga chan za shi zuwa garin ya yi shari’a bissa masu-rai da matatu.
    Ina bada gaakiya ga Ruhu Mai-tsarki: Ekklisiya mai-tsarki Katolika: Zumuntar Tsarkaka: Gafarar zunubi: Tashin jiki, Da rai mara-matuka. Amin.

Malami. Ubangiji shi zamna tare da ku.
Amshi. Tare da ruhunka kuma.

Malami. Mu yi addu’a.

Malami.Ya Ubangiji ka yi mana jinkai.
Amshi. Ya Almasihu ka yi mana jinkai.
Malami. Ya Ubangiji ka yi mana jinkai.
 

Apostles' Creed

ADDU’AR UBANGIJI

    Ubanmu wanda ke chikkin Samma, a tsarkake sunanka, mulkinka shi zo, abin da ka ke so a-yi shi, chikkin duniya kammar yada a-ke yinsa chikkin samma. Ka ba mu rananga abinchin yini. Ka gafarta mana laifinmu, kammar yada muna gafarta ma wadanda su ke yi mamu laifi. Kadda ka kai mu wurin jaraba, amma ka cheche mu dagga Shaitan. Amin.

    Malami. Ya Ubangiji ka bayanna jinkanka bissammu.
    Amshi. Ka ba mu chetonka kuma.
    Malami. Ya Ubangiji ka chechi sarki.
    Amshi. Da jinkai kuma ka ji mu lokachinda muna kirra.
    Malami. Ka chikka masu-bautanka da adilchi.
    Amshi. Jama’arka kuma zababu ka faranta masu uchiya.
    Malami. Ya Ubangiji ka chechi jama’arka.
    Amshi. Ka sa ma gadonka albarka.
    Malami. Ka ba mu kwanuka lafafa.
    Amshi. Gamma babu wanda ke yaki domin mu sai kai kadai Ya Allah.
    Malami. Ya Allah ka tsarkaki zukatanmu dagga chikkinmu.
    Amshi. Kadda ka dauki mana Ruhunka Mai-tsarki.
 

Lord's Prayer

    Ya Allah wanda kai ne ma-farin lafiya, mai-son zumunta kuma, chikkin saninka ranmu na har abada ya tabatta, bautarka yanche chikkake ne; Ka kare mu, mu bayinka kaskantatu dagga dukan falmakin ma-kiyanmu; domin mu da muna dogara ga kariyakka babu tantamma, kadda mu ji tsoron karfin kowanne abokin-gaba, ta wurin ikon Isa Almasihu Ubangijinmu. Amin.

    Ya Ubangiji, Ubanmu na samma, Mai-iko duka, Alla ma-dawami, wanda ya kawo mu farkon yinin nan lafiya, Ka yi mana kariya a-chikkinta da ikonka mai-girma, ka sa kuma yo kadda mu fada chikkin kowanne zunubi, kadda mu yi karrabas da kowanne irin hatseri; amma mu yi dukan al’amuranmu da nufin mulkinka, kullum mu yi abin da shi ke mai-adilchi a-gabbanka, ta wurin Isa Almasihu Ubangijinmu. Amin.

ADDU’AR SARKIN TURE

    Ya Ubangiji, Ubanmu na samma, ma-daukaki, mai-iko, Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji, kai daya ne ma-hukumchin ma-hukumta, dagga kursiyinka kana duban dukan ma-zamnan duniya; da himmar zuchiya muna rokonka, ka dubi Sarkinmu Edward mai-nasiha da alherinka. Ka chikka shi da alherin Ruhunka Mai-tsarki; har kullum shi rika fuskanta ga nufinka, shi bi tafarkinka. Ka yalwatadda shi da baye-bayenka na samma: Ka tsawanta ransa tare de lafiya da wadata. Ka karfafa shi domin shi kada ma-kiyansa, ya yi nassara da su. Akarewa kuma bayan wannan rai shi kai farin-zuchiya mara-iyaka da arziki, ta wurin Isa Almasihu Ubangijinmu. Amin.

ADDU’AR MA-HUKUMTA

    YA Allah mai-yawan nasiha, muna rokonka da tawali’u domin wannan kassa da Governor da Amir na ——, da ma-hukumtan wannan kassa dagga kalkashin sarkinmu mai-ibada mai-nasiha: muna rokonka da yardarka ka bida shawarwarinsu ka albarkache su domin karuwar darajakka, domin albarkar Ekklisiyarka, domin kuma lafiya da girma da alheri na sarkinmu da mulkinsa: ka sa bissa ga aniyassu a-kimtsa al’amura duka, ka kaffa su a-bissa kekyawar tushi mai-karfi, domin lafiya da farin-chikki, gaskiya da shari’a, addini da ibada su tabatta a-wurinmu har tsararaki duka. Wadannan da sauran bukatai duka domin su da mu da Ekklisiyarka duka muna rokonka da tawali’u chikkin suna da ma-tsakkantaka na Isa Almasihu Ubangijinmu da Mai-chetonmu mai-yawan albarka. Amin.
 

Collects

GODIYA TA TAREYA

    Allah Mai-iko duka, uban jejiyankai duka, mu bayinka kasasu, muna yi maka godiya da muminanchi da zuchiya daya, sabada nagartarka da alherinka agaremu da mutane duka. [Bale ga wadannan da su ke so yanzu su yi yabo da godiya sabada jejiyankain da ka yi masu chikkin kwanakim nan.] Muna yabonka domin halitanmu da kiwonmu da dukan albarkar wannan rai; amma gabba da su duka domin kamnarka mai-fi gabban kwatanchi chikkin pansar duniya ta wurin Ubangijinmu Isa Almasihu; domin dalilai na alheri, da begen daraja; mu kwa muna rokonka ka ba mu lura jejiyankanka duka, har zukatanmu su zamma da godiya mai-gaskiya mu bayanna yabonka, ba da bakinmu kadai ba amma da raiyukanmu kuma, muna bada kanmu ga bautarka, muna taffiya gabbanka da tsarki da adilchi dukan kwanakin ranmu, ta wurin Isa Almasihu Ubangijinmu, wanda girma da daukaka gareshi sun tabatta tare da kai da Ruhu Mai-tsarki ba matuka. Amin.

    Ya Allah Mai-iko duka, wanda ya ba mu alheri chikkin wannan lokachi da zuchiya daya my ui maka addu’oïnmu na tareya. Ka yi alkawali kuma lokachinda mutum biyu ko uku sun taru chikkin sunanka za ka ba su rokonsu. Ya Ubangiji ka biya muradin bayinka yanzu da roke-rokensu yanda za ya fi anfaninsu: chikkin duniyan nan kana ba mu sanin gaskiyarka, chikkin duniya mai-zuwa kuma rai har abada. Amin.

    Alherin Ubangijinmu Isa Almasihu, da kamnar Allah, da zumuntar Ruhu Mai-tsarki su zamna tare da mu duka har abada. Amin.


 

General Thanksgiving

Zabura [Psalms 1, 8, 19, 20, 23, 24, 27, 32, 34, 42, 62, 67, 84, 90, 91, 100, 103, 111, 116, 146] pages 14-34
Dokoki goma [10 Commandments], pages 35-36
Wakoki [Hymns] pages 37-48

 


Web author: Charles Wohlers U. S. EnglandScotlandIrelandWalesCanadaWorld